logo

HAUSA

Babbar jakadiyar Sin dake birnin Lagos na Nijeriya ta wallafa sharhi mai taken “Me ya sa yankin Taiwan ba shi da ikon shiga MDD”

2023-09-15 10:55:44 CMG Hausa

A jiya Alhamis da yau Jumma’a, babbar jakadiyar kasar Sin dake birnin Lagos na kudancin tarayyar Nijeriya Yan Yuqing, ta wallafa wani sharhi ta manyan kafofin watsa labaran Nijeriya, ciki hada da jaridar “This Day Live”, da jaridar “Guardian”, da jaridar “Vanguard”, da jaridar “Independent ”, da kuma jaridar “Lagos City Reporters” da sauransu.

Cikin sharhin na ta mai taken “Me ya sa yankin Taiwan ba shi da ikon shiga MDD”, Yan Yuqing ta bayyana cewa, bayan ta kama aiki a matsayin babbar jakadiyar kasar Sin dake birnin Lagos, ya zuwa yanzu watanni 3 ke nan, ita da abokanta dake Nijeriya sun sada zumunci mai zurfi. Kuma a ganinta, al’ummomin Sin da na Nijeriya suna da buri iri daya, a fannin kare ikon mulkin kai da kimar cikakkun yankunan kasa, yayin da suke adawa da duk wanda ke neman raba kan kasa. Lamarin da ya sa, ta yi imanin cewa, tabbas al’ummomin Sin da na Nijeriya za su karfafa fahimtar juna a tsakaninsu, da kuma nuna goyon baya ga juna.

Bayan bude babban taron MDD karo na 78 a kwanan baya, an sake jin muryar “shigar da yankin Taiwan cikin MDD”, don haka Yan Yuqing ke fatan yin bayani ga abokanta a Nijeriya, kan tarihi, da gaskiyar wannan batu.

Ta ce da farko, tun zamanin da da can, yankin Taiwan wani yanki ne cikin kasar Sin, wanda hakan abu ne mai dacewa da doka, wanda aka tabbatar cikin tarihi. Haka kuma, a halin yanzu, kasashen duniya sun amince da manufar “kasar Sin daya tak”, manufar da ta dace da fatan al’umma.

A karshe kuma, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kare ikon mulkin kai da kimar cikakkun yankunan kasa, kuma tabbas za a samu dunkulewar kasar Sin baki daya, a daya bangaren kuma, wadanda suke neman raba kasar Sin ba za su cimma nasara ba. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)