Sin na fatan za a dage takunkuman kashin kai domin samar da damar kyautata ayyukan jin kai
2023-09-15 15:38:39 CMG Hausa
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira da a dage takunkuman kashin kai da wasu kasashe ke kakabawa wasu, ta yadda za a samu zarafin kyautata ayyukan jin kai yadda ya kamata.
Zhang Jun, wanda ya yi kiran yayin zaman muhawara na kwamitin tsaron majalissar da ya gudana a jiya Alhamis, game da bunkasa hadin gwiwa tsakanin sassan gwamnatoci da masu zaman kansu a ayyukan jin kai. Ya ce kakkaba takunkumai na kashin kai ba bisa ka’ida ba, ya yi matukar shafar damar gwamnatocin da ake sanyawa takunkuman, ta samar da muhimman hidimomi, kamar ilimi, da isasshen abinci, kuma hakan yana tasiri ga ayyukan sassa masu zaman kansu a fannonin cinikayya, da zuba jari, da hada hadar kasuwanci, ta yadda hakan ya zamo babban tarnaki ga hadin gwiwa tsakanin sassan gwamnatoci da masu zaman kansu a ayyukan jin kai.
Zhang Jun ya kara da cewa, kamata ya yi sassan kasa da kasa su hada karfi da karfe, wajen kira ga kasashen dake kakabawa wasu takunkuman kashin kai, da su gaggauta janye takunkuman, su kawar da munanan tasirin da hakan ke haifarwa, tare da samar da kyakkyawan yanayin gudanar da ayyukan jin kai a matakin kasa da kasa. (Saminu Alhassan)