logo

HAUSA

Jakadan Sin ya yi kira ga bangarori daban daban da su inganta da kiyaye hakkin dan Adam

2023-09-14 11:27:42 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin Geneve na MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland, jakada Chen Xu, ya ba da jawabinsa a taron kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 54, inda ya yi kira ga bangarori daban daban da su inganta da kiyaye hakkin dan Adam tare, ta yadda za su ba da gudummawarsu ga ci gaban harkokin hakkin dan Adam na duniya.

Chen Xu ya bayyana cewa, kamata ya yi bangarori daban daban su inganta da kiyaye hakkin dan Adam tare yayin da aka cika shekaru 75 da fitar da sanarwar kare hakkin dan Adam na duniya da kuma cika shekaru 30 da fitar da shirin aiki da sanarwar Vienna. 

Chen Xu ya jadadda cewa, Sin ta dade tana bin hanyar bunkasa hakkin dan Adam da ya dace da halin kasarta, kuma ta kawar da talauci karo na farko a cikin tarihinta, aikin kare hakkin dan Adam ya sami babban ci gaba, kuma an kare moriyar al’ummun kabilu daban daban na kasar. 

Kana dokokin tsaron kasa na yankin Hong Kong sun sanya tubali wajen samar da wadata mai dorewa ga yankin. Sin ba ta amince da kowane zargi da ba gaskiya ba, tana fatan ta ba da gudummawarta ga ci gaban harkokin hakkin dan Adam na dunyia tare da sauran kasashen duniya bisa tushen mutunta juna.(Safiyah Ma)