logo

HAUSA

Matasan Amurka bakaken fata sun fi fama da tashin hankali na harbe-harben bindiga

2023-09-14 10:42:58 CMG Hausa

Rukunin ‘yan jarida na Crusader ya rawaito a ranar Talata cewa, a duk fadin Amurka, bakaken fata na yawan mutuwa, ana raunata su ko kuma suna fama da tabin hankali sakamakon rikice-rikice masu nasaba da harbe-harben bindiga.

Rahoton ya ce, "A cewar cibiyar yaki da cututtuka, babban abin da ke haddasa mace-mace a tsakanin yara bakaken fata da kuma matasa masu shekaru 1 zuwa 44 na Amurka, shi ne kisan kai da bindigogi."

Wannan rikicin ya yi illa ga lafiyar kwakkwalwar bakar fata, musamman ta hanyar haddasa tsoro, damuwa da bakin ciki, yayin da masana'antar bindiga ke samun biliyoyin daloli, a cewar rahoton.

Tasirin wannan rikicin ga al'ummar bakar fata ba sabon abu ba ne. Masana sun dade da sanin cewa ‘yan Amurka bakaken fata, kamar dai yadda a cikin mafi yawan wasu kididdigar zamantakewa mai tsoratarwa, suna dauke da radadin sakamakon tashin hankali na harbe-harben bindiga a zahiri da kuma a zuciya, har ma ya nuna cewa wannan matsalar na matukar tasiri ga sakamakon ilimi kamar makin jarrabawa. (Yahaya)