logo

HAUSA

Sin Da Venezuela Sun Inganta Dankon Zumunci A Tsakaninsu

2023-09-14 21:51:32 CMG Hausa

Yayin da kafofin yada labaru na kasashen Latin Amurka suka ba da rahotanni kan yadda shugaban kasar Venezuela Nicolás Maduro ya kammala ziyarar aiki a kasar Sin a ranar 14 ga wata, sun ambato cewa, ziyararsa, ziyara ce mai muhimmanci a tarihi, inda kasashen 2 suka kyautata huldarsu zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, tare da daddale goman yarjejeniyoyin hadin kai.

A shawarwarin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin da shugaba Maduro suka yi a ranar 13 ga wata, Xi ya ce, kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Venezuela, ya cimma burikan jama’arsu duka, kana ya dace da zamani. Kamfanin dillancin labaru na Prensa Latina ya ce, ziyarar Maduro ta wannan karo, ziyara ce da ta samu dimbin sakamako, inda kasashen 2 suka kyautata huldarsu, da ba da sanarwar hadin gwiwa bayan shawarwarin shugabannin 2 da daddale tarkardun hadin gwiwa da dama.

A shekarar 2024 ne, za a cika shekaru 10 da kafa taron dandalin tattaunawar kasar Sin da kasashen Latin Amurka, kana shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Venezuela. Nan gaba kasashen 2 za su habaka hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, a kokarin kara amfanawa jama’arsu da ma hadin gwiwar Sin da kasashen Latin Amurka. (Tasallah Yuan)