logo

HAUSA

Kebe Kai Ba Zai Haifarwa Amurka Da Mai Ido Ba!

2023-09-14 17:05:49 CMG Hausa

Sabuwar samfurin wayar salula da babban kamfanin kere-keren fasahohi na Huawei na kasar Sin ya fitar ba da jimawa ba, ta ja hankalin al’ummun kasar Sin, da ma na sauran sassan duniya. Wayar salular ta kamfanin na Huawei mai dauke da sabbin fasahohin zamani ta kara haskakawa duniya irin ci gaban da kasar Sin ke samu a wannan fanni na kere-keren na’urorin zamani, duk da tarnaki da Amurka ke kakabawa kamfanonin Sin a kai a kai.

Duk da wannan ci gaba, Amurka ta ci gaba da nacewa matsayinta, tana mai bayyana matakanta na “kebe kai” a matsayin dabarar da za ta kai ta ga tudun mun tsira. Amurka ta ci gaba da aiwatar da matakan dakile ci gaban fannin fasaha na Sin, ta hanyar hana shigar da wasu fasahohin kasar zuwa kasar Sin.

To sai dai kuma, dalilai na zahiri sun tabbatar da cewa, irin wadannan matakai da Amurka ke dauka na kebe kai, ba za su haifar mata da nasarar yin babakere ba. Domin kuwa duk wadanda suka rungumi irin wannan hanya da Amurka ta dauka, a karshe za su girbe mummunan sakamako ne kawai.

A shekarun baya bayan nan, gwamnatin Amurka ta sha kakkabawa Sin takunkumai, karkashin manufofin da take cewa na tsaron kasa ne, a wani mataki na haifar da koma baya ga kasar Sin ta fannin ci gaban kimiyya da fasaha.

Alal misali, dokar nan mai lakabin “Dokar kimiyya da sassan laturori na CHIPS" ta jawo cece ku ce mai yawa, duba da yadda Amurka ke amfani da ita wajen hanawa kamfanonin laturorin Sin damar amfani da sassan Chips da ake kerawa a Amurka, wanda hakan ya sabawa ka’idojin gudanar da cinikayya, da hadin gwiwar kamfanoni ba tare da tarnaki ba.

Ko shakka babu, matakan Amurka sun ci karo da manufofin gudanar a hadin gwiwar kimiyya da fasaha a bude, kana a hannu guda, hakan ya nuna yadda Amurka ke kallon kanta a matsayin wadda za ta iya dakile ci gaban kasar Sin a fannonin kirkire-kirkiren fasaha.

Sai dai kuma sabanin tunanin Amurka, idan mun waiwayi tarihi, muna iya ganin cewa, tun asali ci gaban kasar Sin na da alaka ne da karfin kashin kanta, tun daga farko-farkon ci gabanta a fannonin kimiyya da tsaro, har zuwa manyan nasarori da ya cimma a bangaren ayyukan sama jannati, da fasahohin sadarwa masu zurfi, zuwa tsarin fasahar hidimar taswirar BeiDou, da ma fasahar sassan laturori na “chips”. (Saminu Alhassan)