Tianjin: An bude bikin baje kolin jiragen sama masu saukar ungulu na kasa da kasa na kasar Sin karo na 6
2023-09-14 21:47:47 CMG Hausa
Masu kallumu, a bikin baje kolin jiragen sama masu saukar ungulu na kasa da kasa karo n 6 da aka bude yau Alhamis a birnin Tianjin da ke arewacin kasar Sin, kamfanoni sama da 350 sun nuna jiragen sama masu saukar ungulu da jiragen sama maras matuka masu inganci nasu, ciki har da wasu fiye da 40, wadanda wannan ne karo na farko da suka halarci bikin.