logo

HAUSA

Bunkasuwar Sin Wata Dama Ce Ba Kalubale Ba

2023-09-13 19:24:10 CMG Hausa

Bunkasuwar kasar Sin ko kadan ba ta taba zama wata barazana ko kalubale ga duniya ba. Sanin kowane cewa, kasar Sin ta raba fashohinta na yaki da talauci da kwararowar da yaki da ta’addanci bisa doka da rage fitar da gurbatacciyar iska mai illa ga muhalli da sauransu ga sassan duniya.

Wani misali mai muhimmanci shi ne, a lokacin da aka samu bullar annobar COVID-19 a sassan duniya, an ga yadda mahukuntan kasar Sin suka rika raba fasahohi da kayayyakin yaki da annobar da ma ma’aikatan kiwon lafiya zuwa sassan duniya don yakar annobar. Kana a lokacin da ta yi nasarar samar da alluran riga kafin annobar COVID-19, kasar Sin ta raba alluran ga kasashen duniya, matakin dake kara tabbatar da cewa, ci gaban kasar Sin ba barazana ko kalubale ne ga duniya ba.

Kasar Sin ta sha nanata wannan batu a lokuta daban-daban, tare da nuna misali a zahiri, koda a baya-bayan nan ma, firaministan kasar Sin Li Qiang ya shaidawa shugaban kasar Amurka Joe Biden a gun taron kolin kungiyar G20 da aka gudanar a birnin New Delhin kasar India cewa, ci gaban kasar Sin wata dama ce, maimakon kalubale ga kasar Amurka da ma duniya baki daya, don haka ya kamata kasashen biyu su karfafa mu'amala a tsakaninsu.

Kasar Sin, kamar ragowar kasashe na da ikon zabar hanyoyin raya kanta bisa yanayin da take ciki, don haka, bunkasuwar kasar, kamar yadda ta sha nanatawa, har kullum buri da manufar kasar Sin, shi ne tabbatar da ci gaba da zaman lafiyar duniya baki daya, sabanin yadda wasu kasashe ke kallonta da ma yada jita-jitar cewa, wai ci gaban kasar Sin, musamman kokarin da take na zamanantar da kanta, baraza ce ga duniya.

Sanin kowa ne cewa, kasar Sin na da dabaru da fasahohi masu kyau a fannin ingiza zamanintarwa da hadin kan kasa da kasa, da sa kaimi ga canja salon makamashi, kuma dukkansu abin koyi ne ga kasashen duniya. Amma wasu kasashe na nuna kishi da ci gaban kasar Sin, inda suke kokarin yiwa wannan ci gaba bahaguwar fahimta tare da neman hana ci gabanta ta kowa ce hanya.

Har kullum kasar tana fatan kasashen yammacin duniya, za su kalli ci gabanta, da kokarin da take na zamanantar da kanta da idon basira, ta yadda za su dakatar da yada farfaganda maras tushe, ta daukar wannan manufa da masu fashin baki ke cewa, za ta amfani duniya a matsayin barazana. Masu iya Magana dai na cewa, zakaran da Allah na nufa da cara ko ana muzuru ko ana shaho sai ya yi. (Ibrahim Yaya)