logo

HAUSA

Ma’aikatan jin kai na MDD sun nemi karin kudade don yaki da tamowa a arewa maso gabashin Najeriya

2023-09-13 10:32:43 CMG Hausa

Ma’aikatan jin kai na majalisar dinkin duniya sun bayyana a ranar Talata cewa yara ‘yan kasa da shekaru biyar 700,000 a yankin arewa maso gabashin Najeriya ke fuskantar matsanancin rashin abinci mai gina jiki, adadin da ya ninka na shekarar 2022.

Majalisar dinkin duniya da abokan hulda a Najeriya na neman karin kudade domin kara kai daukin jin kai a lokacin rani da kuma magance matsalar karancin abinci da abinci mai gina jiki a jihohin Adamawa, Borno da Yobe, a cewar ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD (OCHA). Yaran da matsalar tamowa ke yi wa barazana na daga cikin mutane miliyan 4.3 da ke fuskantar barazanar matsananciyar yunwa.

A watan Mayu, majalisar dinkin duniya da abokan hulda a Najeriya sun yi kira da a ba su kusan dalar Amurka miliyan 400 don magance matsalolin da suka fi tsanani a jihohin uku har zuwa watan Satumba. Duk da haka, kudin da suka samu kadan ya haura miliyan 200. (Yahaya)