logo

HAUSA

Muhimmancin sabbin fasahohin zamani ga ci gaban rayuwar bil-Adam

2023-09-13 08:50:54 CMG Hausa

A wannan makon ne, aka shirya dandalin kirkire-kirkire na Pujiang na shekarar 2023 a birnin Shanghai na kasar Sin.

A cikin wasikar taya murna da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aikewa dandalin ya bayyana cewa, a yau duniya tana fuskantar sauye-sauye cikin sauri da ba a taba ganin irinsa ba a cikin karni, kuma ana samun sabon zagaye na juyin juya hali a fannin kimiyya da fasaha da sauye-sauyen masana'antu.

Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da bin dabarun bude kofa ga kasashen waje da samun moriyar juna, da ci gaba da fadada bude kofa ga kasashen waje, da inganta mu'amalar kimiyya da fasaha ta kasa da kasa, da ma yin hadin gwiwa, da zuciya guda, da fito da karin matakai daban daban, da gina tsarin muhallin takara na kirkire-kirkire na duniya mai adalci maras gurbata muhalli, da yin aiki tare da sauran kasashe, wajen samar da yanayi mai bude kofa, da adalci, da rashin nuna wariya ga ci gaban kimiyya da fasaha.

Ana sa ran dandalin kirkire-kirkire na Pujiang ya kiyaye taken kirkire-kirkire, da zaburar da sabbin dabaru, da yada sabbin tunani, da kara inganta ruhin kirkire-kirkire, da samar da sabbin gudummawa wajen ciyar da hadin gwiwar kasa da kasa a fannin kimiyya da fasaha gaba, da inganta rayuwar daukacin bil Adama.

Bayanai na nuna cewa, an inganta sama da kilomita 3,500 na titunan kasar Sin da fasahohin zamani. Kana tun bayan shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, an samu nasarori a fannin samar da sabbin ingantattun ababen more rayuwa, tare da zurfafa amfani da fasahohin sadarwa kamar tsarin taurarin dan Adam na Beidou da 5G, haka kuma ingancin hidimomin sufuri na ci gaba da karuwa, baya ga samun kakkyawan sakamako a fannin sa ido kan karfafa masana’antar fasahohin zamani. Wadannan a cewar masana, wani bangare na ci gaban sabbin fasahohi na zamani. (Saminu, Ibrahim, Sanusi Chen)