logo

HAUSA

Wakilin Sin: Ya zama dole Japan ta amince da sa ido daga kasa da kasa

2023-09-13 10:58:00 CMG Hausa

A wajen taron ‘yan majalisar hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA na watan Satumbar bana, Li Song, zaunannen wakilin kasar Sin dake Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa a birnin Vienna na kasar Austria, ya yi kakkausar suka kan kaddamar da shirin zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku da kasar Japan ta yi a gefe guda, inda kuma ya bukaci kasar da ta amince da sa ido sosai daga kasashen duniya.

Jami’in ya ce, a ranar 24 ga watan Agusta, gwamnatin Japan ta kaddamar da aikin zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, ba tare da la’akari da babbar adawa da shakkun kasa da kasa ba. Tarihi ba zai manta da ranar ba. Zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, babbar matsala ce dake shafar tsaron amfani da makamashin nukiliya, wadda ke iya haifar da illa ga kasashe daban-daban kuma cikin dogon lokaci, wato ba harka ce ta ita Japan kadai ba. Hatsarin yoyon nukiliya a tashar makamashin nukiliya ta yankin Fukushima dake kasar Japan, wanda ya wakana shekaru 12 da suka gabata, ya riga ya haifar da babbar barna. Don haka Japan na da hakki da nauyin daidaita ruwan dagwalon nukiliya, ta hanya mafi dacewa da tsaro, maimakon kara haifar da illa ga muhallin yankunan teku da lafiyar al’ummun kasa da kasa. Zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku, ba zabi kadai ba ne, kana, ba zabi ne mafi tsaro da dacewa ba. (Murtala Zhang)