logo

HAUSA

Majalissar wakilan Amurka ta yi kira da a kaddamar da bincike game da yiwuwar tsige shugaba Biden

2023-09-13 10:23:57 CMG Hausa

Kakakin Majalisar wakilan Amurka daga jam’iyyar Republican Kevin McCarthy, ya yi kira da a kaddamar da bincike game da yiwuwar tsige shugaban kasar mai ci na jam’iyyar Democratic Joe Biden.

McCarthy wanda ya yi kiran a jiya Talata, ya ce bukatar hakan ta biyo bayan wasu zarge zarge ne masu nasaba da cin hanci, da ake dangantawa da iyalan gidan shugaba Biden, a gabar da ’yan jam’iyyar Republican ke binciken hada hadar kasuwancin dansa Hunter, tun kafin mista Biden ya kama aiki a matsayin shugaban Amurka a shekarar 2021.

Ya ce, "Wadannan zarge-zarge sun nuna dabi’ar cin amanar mukamin da shugaban ke rike da shi, da dakile bincike, da cin hanci", matakin da ya sa majalissar ta wakilai ke burin kara zurfafa bincike. (Saminu Alhassan)