logo

HAUSA

Za a samar da dubban murhunan girki irin na zamani a jihar Bauchi domin rage dumamar yanayi

2023-09-13 09:20:05 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Bauchi dake arewa maso gabashin Najeriya za ta hada karfin da wata kungiya mai zaman kanta wajen samar da dubban murhunan girki domin sayarwa kan farashi mai sauki ga al’ummar jihar a wani mataki na dakile karuwar matsalar gurbar muhalli.

Yayin wani taron wayar da kai da kungiyar ta shiryawa sarakuna da kungiyoyin al’umma a garin Bauchi, kungiyar mai suna Clean, Cooking, Forestry & Safe Water ta ce, ta lura jihar Bauchi na daga cikin jahohin da ake yawan sare itatuwa domin girki a Najeriya, lamarin da yake haifar da dumamar yanayi a kasar baki daya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.####

Mr. Joel Haruna yana daya daga cikin jagororin wannan kungiya, ya ce, hakika akwai fa’idoji masu yawan gaske da za a samu ta hanyar amfani da sabbin nau’inkan murahun girkin.

"Manufar wannan taron shi ne domin a wayar da kan jama’a muhimmancin amfani da wadannan murhuna da aka kawo domin ya taimaka wajen rage hayaki, da kuma hayakin zai kawo damuwa ga lafiyar mata da yara dake gun girki, sannan kuma mu tabbatar da yadda za a samu ruwan sha wanda zai kawo lafiya ga jama’a yayin da suke sha, wannan murhu da muka kawo yana rage hayakin, kuma yana nuna cewa idan a baya mutum na amfani da gawayi kilo 10 wajen girki, zai ragu zuwa biyar ko hudu idan an yi amfani da wannan murhu.”

Ita kuwa Madam Lydian Joshua, darakta janaral ta hukumar cimma muradun karni SDG ta Najeriya reshen jihar Bauchi ta ce, hakika yawan sare dazuzzuka wurin na zama fili, zai zama babbar illa a gaba musamman ga yara masu tasowa za su iya rayuwa cikin kunchin muhalli, wannan shi ne dalilin da ya sa aka gabatar da wannan sabuwar fasahar murhun girki.

“Kuma ni yadda na san mai girma gwamna na jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Kauran Bauchi yana jin wannan tsari tare da uwargidansa Dr Lami Bala Muhammed, za su karbe shi hannu bibbiyu, tare da shi kwamashina na muhalli, kuma da maganar tsaftace muhalli da maganar ruwa na san ya zo da kishin haka, shi ya sa daga zuwansa aka yi kokarin kara habaka sha’anin samar da ruwa ta hannun bankin duniya, don haka muna sa zuciya wadannan abubuwa da muka koya a yau, da ilimi da muka bayar a kan SDG’s zai zama mai amfani kwarai da gaske domin ci gaban al’ummarmu na Bauchi.” (Garba Abdullahi Bagwai)