Abdulkadir Bello: Na karu sosai ta hanyar samun horo a kasar Sin
2023-09-12 15:36:48 CMG Hausa
Abdulkadir Bello, dan Najeriya ne dake aiki a wani kamfanin sadarwar kasar. Kwanan nan ya shigo kasar Sin don samun horo na wasu kwanaki a harkokin sadarwar zamani, bisa hadin-gwiwar kamfaninsa da shahararren kamfanin sadarwar kasar Sin wato Huawei.
A wata hirar da ya yi da Murtala Zhang, malam Abdulkadir Bello ya yi karin haske kan ziyarar aikinsa a kasar Sin a wannan karo, da yadda ya ga wasu wuraren kasar gami da al’ummarta a fannoni daban-daban.
Abdulkadir Bello ya kuma ce ilimin da ya samu a kasar Sin zai kara kyautata ayyukansa a nan gaba, kuma zai yi kokarin koya wa sauran abokan aikinsa ilmomin. (Murtala Zhang)