logo

HAUSA

Shin An Dauki Darasi Daga Harin 9·11?

2023-09-12 17:25:57 CMG Hausa

Yayin da ake cika shekaru 22 da harin ranar 11 ga watan Satumban 2001, har yanzu zukata na kona duba da dimbin asarar rayuka da dukiyoyi da aka samu a wannan rana da ba za a manta da ita a tarihi ba.

Babu wani mai hankali da zai goyi bayan rashin imanin da aka aikata a wannan rana, amma kuma, bai zama wata dama ta farwa mutanen da ba su-ji-ba-su gani-ba. Idan ba a manta ba, dalilin wannan hari ne Amurka ta girke dakarunta tare da mamaye kasar Afghanistan a watan Oktoban 2001. Sai dai, maimakon dakile kungiyar mayakan da take zargi da kaddamar da wadancan munanan hare-hare, illar da ta haifar cikin shekaru 20 da ta shafe tana yaki a kasar ya shafe duk wani dalili da take ikirarinta na da shi.

Yaki da ta’addanci abu ne mai kyau da kowa yake goyon baya, sai dai nuna fin karfi kan marasa karfi, cin zali ne, kuma shi ma wani nau’i ne na ta’addanci. Matakin Amurka ya haifar da mummunar asara maimakon gyara, haka kuma ita kanta ba ta tsira daga jin radadin abun da ta yi ba.

Na kan yi mamakin yadda Amurka ta keta dokokin kasa da kasa da cikakken ’yancin Afghanistan da sunan yaki da ta’addanci, amma take ganin baiken kasar Sin da bata mata suna don ta yaki ta’addanci da kare cikakken ’yanci da ikonta ta hanyoyi mafi dacewa, kuma bisa doka da suka haifar da nasarorin da Amurka ba ta samu ba cikin shekaru 20 da ta yi tana yaki da Taliban.

Da alama har yanzu, Amurka ba ta farga ta dauki darasi ba, bayan shafe shekaru 20 tana yaki, yanzu ’yan Taliban din ne ke mulkin kasar Afghanistan, shin wani alfanu Amurka ta samu? Makudan kudin da ta zuba wajen yaki da Afghanistan sun isa su aiwatar da manyan ayyukan ci gaban al’umma da inganta karfinta na kare kanta. Amma maimakon mayar da hankali kan raya kanta, ta ci gaba da tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe masu cikakken ’yanci da ingiza yaki da rikice-rikice a sassan duniya. (Fa’iza Mustapha)