logo

HAUSA

MDD ta yi Allah wadai da hare hare kan kasuwa dake birnin Khartoum

2023-09-12 10:47:19 CMG Hausa

Shugaban ofishin tsare tsaren ayyukan jin kai na MDD dake kasar Sudan Clementine Nkweta-Salami, ya yi tir da hare haren da aka kaddamar a ranar Lahadi, a wata kasuwa dake birnin Khartoum, lamarin da ya sabbaba kisan fararen hula 40, tare da jikkata wasu da dama. Nkweta-Salami, ya ce ba za a taba amincewa da wannan ta’asa ba, kuma hakan ya sabawa dokokin jin kai na kasa da kasa. Jami’in ya bayyana damuwar sa game da hare haren ne ta shafin sa na manhajar X, wanda a baya aka fi sani da Tiwita.

Tuni dai kwamitin ‘yan gwagwarmaya na kudancin Khartoum, ya zargi dakarun gwamnati ko SAF, da kaddamar da hari kan kasuwar dake kudancin birnin Khartoum, kana kwamitin ya gabatar da hotunan gawawwakin wadanda ya ce harin ya rutsa da su. To sai dai kuma dakarun SAF sun musanta hakan, suna musu cewa ba su taba kai hari kan fararen hula ba.

A daya bangaren kuma, shugaban ofishin tsare tsaren ayyukan jin kai na MDD ko OCHA, kana mataimakin babban sakataren majalissar mista Martin Griffiths, ya ce ya zanta da shugaban rundunar ko ta kwana ta Sudan Mohamed Hamdan Dagalo a ranar Lahadi, inda Griffiths din ya jaddada bukatar samar da damar tallafawa mutanen dake cikin yanayin matsi a kasar, ko da yake ba su tabo batun harin kasuwar ba. (Saminu Alhassan)