logo

HAUSA

Emmanuel Macron: Faransa na tattaunawa ne kadai da halastacciyar gwamnatin Nijar kan batun daidaita sojojin Faransa dake kasar

2023-09-11 11:41:16 CMG Hausa

Bisa rahoton da kafar watsa labarai ta Faransa ta fitar, an ce, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana a birnin New Delhi, babban birnin Indiya cewa, kasarsa na tattaunawa ne kadai da halastacciyar gwamnatin Nijar, game da daidaita sojojin Faransa dake kasar, a maimakon sojojin da suka yi juyin mulki. 

Rahotanni na cewa, a halin yanzu, yawan sojojin Faransa dake Nijer ya kai kusan 1500. Tun daga ranar 2 ga watan nan, dubban al’ummun Nijar sun rika dafifi a gaban sansanin sojojin Faransa dake kudancin birnin Niamey, babban birnin kasar, inda suka yi kiraye-kirayen ficewar sojojin Faransan daga Niamey ba tare da wani sharadi ba. 

Ban da wannan, wata kafar yada labaran Faransa ta labarta cewa, a baya-bayan nan hukumar soja ta Faransa da mahukuntan soja na Nijar sun taba tattaunawa kan batun janye wasu kayayyakin soja na Faransa daga jamhuriyar Nijar. (Safiyah Ma)