logo

HAUSA

Me Shigar AU Cikin G20 Za Ta Kawo Wa Duniya?

2023-09-11 20:14:17 CMG Hausa

An rufe taron kolin kungiyar G20 a New Delhi jiya Lahadi, inda aka amince da gayyatar kungiyar Tarayyar Afirka AU shiga cikin kungiyar a hukumance. Kungiyar Tarayyar Afirka ta zama kungiya ta biyu da ta shiga kungiyar G20 bayan kungiyar Tarayyar Turai.

Yayin da tattalin arzikin Afirka ke ci gaba da dunkulewa a duniya, Afirka suna kara shiga al’amuran kasa da kasa. Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen kara azama kan shigar da AU cikin kungiyar G20. Kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan goyon bayan AU shiga cikin kungiyar G20, saboda su abokai ne da ke amincewa da juna ta fuskar siyasa kan hanyar raya kasa, kana Afirka na taka muhimmiyar rawa a duniya, wadda yake kiyaye adalci a duniya. Shigar da AU cikin kungiyar G20, babbar nasara ce wajen tabbatar da duniya mai ba da damar cudanyar sassa daban daban.

Yanzu nahiyar Afirka ta gaggauta gina yankin cinikin cikin ‘yanci. Bayan shiga cikin kungiyar ta G20, kasashen Afirka za su samu muhimmiyar hanyar tuntubar manyan rukunonin tattalin arzikin duniya dangane da manufofin hada-hadar kudi. Lamarin da zai amfana wa kasashen Afirka wajen tinkarar kalubalolin da suke fuskanta.

Kafin wannan kuma, an shigar da wasu kasashe cikin tsarin hadin kan BRICS. Shigar da AU cikin G20, wani muhimmin batu ne a fannin kara karfin kasashe masu tasowa. Yayin da ake fuskantar sauye-sauye da tashin hankali a duniya, yadda kasashe masu tasowa suke kara fito da muryarsu, ya kara karfin wadanda suke rungumar manufar cudanyar sassa daban daban, hakan zai dakile danniya da siyasar fin karfi.(Tasallah Yuan)