logo

HAUSA

Yadda Kyawawan Al’adu Ke Haskaka Makomar Raya Zamanintarwa Irin Na Kasar Sin

2023-09-11 20:02:56 CMG Hausa

Al’adar iyali tana nufin ka’idar iyali, wanda kuma dabi’a ce da aka gada daga iyalai dattawa ta hanyar kalmominsu da ayyukansu. Samuwar al'adar iyali ta samo asali ne daga dabi'un iyali, al'adun gargajiya, da darussan da aka koya daga tsararraki. Muhimmancin al'adar iyali shi ne zai iya yin tasiri mai zurfi a kan 'yan uwa da kuma taka rawa mai kyau kan ci gaban iyali da al'umma yadda ya kamata.

Da farko, kyakkyawar al'adar iyali na iya kiyaye jituwa da kwanciyar hankali na iyali. A cikin iyali da ke cike da mutunta juna, fahimtar juna da kulawa, dangantakar da ke tsakanin 'yan uwa ta fi dacewa. Irin wannan iyali na iya haifar da yanayi mai dorewa da jin dadi, wanda kuma yana taka muhimmiyar rawa a lafiyar jiki da tunanin ’yan uwa.

Na biyu, al'adar iyali mai kyau na iya samar da kyakkyawan yanayin girma ga yara. A karkashin tasirin al'adun iyali, yara sun fi iya samun ilimi mai kyau da habaka dabi’a masu kyau. Wannan yana da matukar fa'ida ga girmansu.

A karshe, al'adar iyali kuma tana da matukar mahimmanci ga gadon dabi'a da al'adu na zamantakewa. Yayin da 'yan uwa ke ci gaba da yin biyayya ga al'adar iyali, al'adun iyali su ma suna yaduwa a hankali. Irin tsarin gado daga kaka da kakani, zai sa a sami kwarin gwiwa da alfahari ga wadanda suka gaji al'adun iyali, wannan ba wai kawai yana nufin mutuncin iyali ba ne, har ma abin gado mai daraja ga al'umma baki daya.

Don haka, ya kamata kowannenmu ya kiyaye al'adar iyali, ya gaji al'adun iyali, ya ba da gudummawa ga ci gaban al'umma.

Tun shekaru fiye da dubu biyu da suka wuce, mai hikima Confucius ya ba da fifiko kan koyon ilmi, har ma ya zama abin koyi wanda ya cancanci a koya har abada. Ra’ayin da Confucius ya assasa, da akidun da ya bunkasa bisa wannan tunani, sun yi tasiri sosai ga wayewar kan kasar Sin.

A watan Satumba na shekarar 2014, a yayin bikin bude taron tattaunawa na kasa da kasa na tunawa da cika shekaru 2565 da haihuwar Confucius, da kuma babban taro na biyar na kungiyar akidun Confucius ta kasa da kasa, Xi Jinping ya nakalto layin farko na Tsararren Kundin Kalmomi da Akidun Confucius dake cewa, "Abin farin ciki ne samun abokai daga nesa", don maraba da mahalarta taron daga kasashe daban daban.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, akidun Confucius, da sauran akidu da al'adu da aka samar a lokacin kafuwar al'ummar kasar Sin, da ci gaban al'ummar kasar, sun zayyana yadda Sinawa ke gudanar da ayyuka a fannin ruhi, da tunaninsu da hankali, da nasarorin da suka cimma a fannin al'adu a fafutukar gina kasarsu tun zamanin da. Hakan na nuni da yadda al'ummar kasar Sin ke amfani da ruhi, kuma muhimmin abu ga al'ummar kasar wajen samun bunkasuwa.

Bisa la'akari da umurnin shugaban kasar, tsohon birnin Qufu ya kebe wuraren "Tsohon Confucius uku" wato Gidan Confucius, da Gidan Ibada na Confucius, da kuma Kaburburan Confucius da Iyalansa a matsayin mafari, kuma ya kara da "Sabbin wuraren Confucius Uku" da suka hada da Kwalejin Nazarin Confucius, Gidan Tarihi na Confucius, da Nishan Mai Tsarki wato wurin da aka haifi Confucius, don inganta al'adun kasar Sin, da kara ilimantar da jama’a game da wannan falsafa a sabon zamani.

A shekarar 1994, Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wuraren "Confucius Uku" wato Gidan Confucius, da Gidan Ibada na Confucius, da kuma Kaburburan Confucius da Iyalansa a cikin jerin abubuwan tarihi na duniya.

"Idan kuna son kara fahimtar kasar Sin, ya kamata ku fara fahimtar Confucius, idan kuna son kara fahimtar Confucius, dole ne ku ziyarci wuraren 'Confucius uku'." Yang Chaoming, tsohon shugaban Kwalejin Nazarin Confucius, kuma fitaccen farfesa na kwalejin nazarin akidun Confucius na jami'ar Shandong, ya bayyana cewa, al'adun da Confucius ya kafa, wani muhimmin bangare ne na al'adun gargajiyar kasar Sin. Akidar da Confucius ya gabatar ta "kauna, aminci, ladabi, hikima, da mutunci" har yanzu su ne ruhin al'ummar Sinawa.

“Ya kamata a rika nuna gaskiya a lokacin da ake mu’amala da abokai”, “Idan ka hadu da mutumin kirki, to, kamata ya yi ka yi kokarin zama kamarsa, idan ka gamu da akasin haka, sai ka yi tunani ko kai ma kana da irin wannan rauni”…… Tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, Xi Jinping ya dora muhimmanci sosai kan gadon al'adun kasar Sin, da dorewar wayewar kan Sinawa. Ya jaddada cewa, "Dole ne mu mai da hankali kan kare da gadon tarihi da al'adu, da kuma kare tushen ruhin al'ummar Sinawa." Ya sha ba da misali da wasu litattafan gargajiya na Confucius, ciki har da Tsararren Kundin Kalmomi da Akidun Confucius a lokuta daban-daban, inda ya koyi hikima daga kyawawan al'adun gargajiya na kasar Sin wajen gudanar da mulkin kasa.

A yau, jama'a sun bi sahun Xi Jinping wajen ziyartar Gidan Confucius mai girman eka 240, lamarin dake kara nuna karfin al’adu.

Mataimakin daraktan kamfanin ba da hidimar yawon shakatawa ta al’adun Confucius na birnin Qufu mista Zhang Lei ya bayyana cewa, "Tun daga farkon wannan shekarar, yawan masu yawon bude ido da suka ziyarci wuraren shakatawa na 'Confucius Uku' ya karu sosai, inda ya kai miliyan 3.6, wanda hakan ya sa shi zama wurin binciken al'adun gargajiya mai muhimmanci."

A kan hanyar zuwa kabarin Confucius, akwai Kwalejin Nazarin Confucius, wato daya daga cikin sabbin “Confucius Uku”. A shekarar 1996, Majalisar Gudanarwar Kasar Sin ta amince da kafa Kwalejin Nazarin Confucius a matsayin hukumar musamman ta nazarin akidun Confucius.

A yayin binciken da ya gudanar a Qufu, Xi Jinping ya nuna cewa, ya kamata a martaba matsayin reshen falsafa dake nuna abubuwa a zahiri ne kadai suka fito daga halittu a yayin da ake nazarin Confucius da akidunsa, ta yadda za a yi amfani da abubuwan da suka gabata don zama darasi, da kawar da rashin gaskiya, da zurfafa nazari, ta yadda zai taka rawar gani a sabon zamanin da muke ciki.

A cikin 'yan shekarun nan, Kwalejin Nazarin Confucius ya samar da jerin sakamakon bincike mai tasiri ga duniya. Musamman ma, aikin "Fassara Sin" da ya shafe shekaru 6 yana yi, wanda masana ilimin Confucius ke jagoranta.

A sa'i daya kuma, an fassara wasu littattafan game da Confucius da ke jawo hankalin Xi Jinping zuwa harsuna 16 da suka hada da Turanci da Jamusanci da yaren Koriya ta Kudu da dai sauransu, kuma sun karade kasashe fiye da 10 kamar Amurka, da Koriya ta Kudu, da Kyrgyzstan, kuma an buga fiye da kwafi dubu 500.

Wuraren “Confucius Uku” tsoffi da sabbi sun kunshi abubuwan da suka gabata da kuma nan gaba, kuma sun zama wata gadar dake haskaka da inganta yin kirkire-kirkire kan sauye-sauye da raya kyawawan al'adun gargajiya na kasar Sin.