logo

HAUSA

Gwamnonin jihohin arewa maso gabashin Najeriya sun koka kan karuwar ayyukan ’yan ta’adda a yankin

2023-09-11 10:18:55 CMG Hausa

Kungiyar gwamnonin jihohin dake arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana damuwa bisa rahotannin karuwar hare-haren ’yan ta’adda a wasu sassan jihohin dake shiyyar.

Sun bayyana wannan damuwa ce a yayin taronsu karo na 8 da suka gudanar a birnin Maiduguri a karshen makon jiya, a game da haka kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya ta gaggauta kaiwa yankin dauki.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kamar yadda yake kunshe cikin takardar sanarwar bayan taron wadda take dauke da sa hannun shugaban kungiyar, kuma gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum, kungiyar ta ce irin wadannan ’yan ta’adda su ne wadanda tun farko sojoji suka fatattaka daga wasu sassan kasar, amma yanzu kuma sun yi kaura zuwa jihohin Bauchi, Gombe da kuma Taraba inda suke ci gaba da aikata muggan ayyukansu.

Haka kuma kungiyar gwamnonin ta bayyana cewa tana sane da yadda wasu sarakuna da shugabannin al’umomi a shiyyar ke hada baki da ’yan ta’adda ta hanyar ba su mafaka a duk lokacin da suka aikata ta’addanci a shiyyar.

A sakamakon hakan kungiyar gwamnonin ta amince da murya guda wajen zartar da hukunci mai tsanani ga duk wani  basarake  ko  jagoran al’umma da ya hada baki da ’yan ta’adda wajen haifar da cikas ga zaman lafiyar shiyyar.

A lokacin da yake bude taron, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce, batun ci gaba da wanzar da yanayin zaman lafiya a kasa baki daya yana daga cikin burikan wannan gwamnati, inda ya kara da cewa:

“A sakamakon rahoton bayan tashe-tashen hankula da kididdigar asarar da aka yi da kuma kokarin gina tabbataccen ginshikin zaman lafiya wanda aka gudanar bisa hadin gwiwa da Bankin Duniya da kungiyar tarayyar Turai da kuma fadar shugaban kasa, an gano cewa, kungiyar Boko Haram ta haifar da barnar da aka kiyasta ya kai dala biliyan 9 a shiyyar arewa maso gabas.” (Garba Abdullahi Bagwai)