logo

HAUSA

Karnuka na gane idan iyayen gijinsu suna cikin damuwa

2023-09-10 17:42:17 CMG Hausa

 

Wani nazari da aka gudanar a kasar Birtaniya ya nuna cewa, bayan da aka horas da karnuka, suna iya ganewa ta hanyar numfashi, idan iyayen gijinsu suna cikin damuwa.

Kafar rediyon kasar Birtaniya wato BBC ya ruwaito cewa, masu nazari daga jami’ar Queen's University Belfast ta Birtaniya, sun gayyaci masu aikin sa kai 36, da su kammala ayyukan ilmin lissafi masu wuya cikin gejeren lokaci. Kuma muddin suka yi kuskure, to, za a dakatar da su nan take tare da sanar da su. Masu nazarin sun tattara bayanai dangane da bugun zuciya, da hawan jini, da sauran bayanan da suka bayyana matsin lambar da ake fuskanta, kafin masu aikin sa kan sun fara ayyukan, da kuma bayan sun kammala ayyukan, da kuma samfur din iskar da masu aikin sa kan suke numfashin ta da kuma guminsu.

Ban da wannan kuma, masu nazarin sun horas da karnuka 20, dabarun bambance samfur din iskar da masu aikin sa kan suke yin numfashin ta, da guminsu bayan da suka samu matsin lamba. A karshe dai wasu 4 daga karnukan sun yi fice sosai. A cikin jarrabawar da aka gudanar har sau dari 7, wadannan karnuka 4, sun samu nasara har sau fiye da 650, wajen bambance samfurin iskar da masu aikin sa kan suka yi numfashin ta, da guminsu bayan da suka samu matsin lamba.

A baya, akwai wasu shaidu da ke nuna cewa, ta hanyar numfashi ne, karnuka ke gane idan wasu mutane sun kamu da wasu cututtuka. Masu nazarin da suka gudanar da binciken sun yi karin bayani da cewa, sakamakon nazarinsu ya nuna cewa, warin da dan Adam kan fitar yayin da yake cikin nutsuwa, da kuma lokacin da yake fuskantar babban matsin lamba sun sha bamban da juna. Don haka karnuka sukan gane idan mutane suna fuskantar babban matsin lamba.

Dangane da sakamakon nazarin, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijiing, ta yi karin haske da cewa, idan an horas da karnuka kamar yadda masu nazarin suka yi, a kokarin ganin karnukan sun gane idan masu fama da ciwo suna fuskantar babban matsin lamba, to, karnukan za su iya taimakawa masu fama da ciwon. (Tasallah Yuan)