logo

HAUSA

Mutane sama da dubu biyu ne suka mutu sanadiyar girgizar kasar da ta auku a Morocco

2023-09-10 16:53:05 CMG Hausa

 

A ranar Jumma’a da dare ne, wata girgizar kasa mai karfin gaske ta auku a kasar Morocco, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu biyu, ana kuma saran wannan adadin zai karu, a yayin da masu aikin ceto ke kokarin isa yankunan da iftila’in ya fi shafa.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana alhininsa game da asarar rayuka da aka samu sakamakon girgizar kasar, kamar yadda kakakinsa ya bayyana jiya Asabar.

Kafofin watsa labaran kasar sun ruwaito cewa, girgizar kasar mai karfin maki 6.8, ta afku a kasar Morocco a ranar Juma'a da karfe 11 da mintuna 11 na dare agogon kasar, a zurfin kilomita 18.5. Kuma adadin wadanda suka mutu ya kai 2,012.

A jiya Asabar, kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta sanar da cewa, za ta baiwa kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar Morocco taimakon gaggawa na tsabar kudi har dalar Amurka dubu 200, domin gudanar da ayyukan ceto.(Ibrahim)