logo

HAUSA

An dakatar da aikin hakar ma’adinai a jihar Neja ta Najeriya

2023-09-10 15:21:09 CMG Hausa

Mahukunta a jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya sun sanar da dakatar da aikin hakar ma’adanai a fadin jihar baki daya.

Kwamashinan harkokin ma’adinai na jihar Alhaji Garba Sabo Yahaya ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya ce, gwamnatin jihar ta dauki wannan mataki ne domin ta tantance kamfanonin hakar ma’adinai tare kuma da inganta sha’anin harkokin kudaden shiga.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Kwamishinan harkokin ma’adinai ta jihar Neja ya ce, sakamakon yanayin tsaro da ake ciki a jihar, wajibi ne gwamnati ta matsa kaimi wajen lura da hada-hadar masu hakar ma’adinai, kasancewar bincike ya nuna cewa, akwai ‘yan ta’adda da dama da suka shiga hakar domin samun kudaden sayen makamai.

Baya ga haka kuma, Alhaji Garba Sabo Yahaya ya ce, gwamnati ba ta samu kudaden shiga da suka kamata daga wajen masu hakar ma’adinan nan, alhali kuwa wannan ita ce hanya mafi girma ta jihar ke samun kudaden shiga wadanda su ne kuma take samun sukunin gudanar da ayyukan raya kasa.

“Gwamna ya ba mu umarnin duk inda ake hakar zinare ba bisa ka’ida ba da su kansu wadanda suke haka bisa doka, dole mu bincika, mu ga wa ke da lasin na ainihi, saboda ba shi yiwuwa a ce kana cikin jiha, wani ya zo yana hakar ma’adinai, amma ba ka san daga inda yake ba, ba ka san ko shi waye ba. Muna son mu bude masu rijista domin mu samu cikakken adadin yawansu, idan aka yi wannan to za ka iya gane masu hakar ma’adinai nawa ake da su a Kwantagora nawa ne ke Shiroro, wannan doka an ce an dakatar, ba wai an ce an tsayar ba ne.”

Muhammed S.D. Manbo shi ne shugaban kungiyar masu hakar ma’adinai a jihar Neja.

“Muna goyon bayan wannan doka da gwamna ya fito da shi, saboda babu yadda za a ce a ma’aikata a jiha ana aiki, amma a ce ba’a san su waye ke aiki ba ko da gwamnatin tarayyar ce ke ba da wannan lasisi. Kamata ya yi a ce gwamnatin jiha na da hurumi a kan wannan al’amari. A cikin dalilan da aka bayar harda batun tsaro, batun tsaron mun san da shi, ni yanzu ko kudi ka ajiye mun, ka ajiye mun jirgin sama, akwai wuraren da in ka ce in je, ni karan kai na ba zan je ba.” (Garba Abdullahi Bagwai)