logo

HAUSA

Sin da Afirka ta Kudu sun daddale yarjejeniya kan shirin binciken duniyar wata

2023-09-09 17:13:42 CMG

Hukumomin kula da sararin samaniyar Sin da Afirka ta Kudu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwar shirin tashar binciken duniyar wata ta kasa da kasa (ILRS), a cewar hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin (CNSA).

Sanarwar ta ce, halarcin kasar Afirka ta Kudu, ya nuna hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu ya zarce daga sararin samaniyar duniya zuwa duniyar wata da zurfafa binciken sararin samaniya tare, wanda zai taimaka wajen ci gaban kimiyya da fasaha a tsakanin kasashen biyu.

Bangarorin biyu za su gudanar da hadin gwiwa mai zurfi, wajen aiwatarwa, da gudanar da aikin injiniya, da aikace-aikace, ilimi da horarwa na ILRS. (Yahaya)