logo

HAUSA

Kai karar gwamnatin Japan gaban kotu da al’ummar kasar suka yi saboda zubar da ruwan dagwalon nukilya a cikin teku mafari ne kawai

2023-09-09 16:38:42 CMG Hausa

Jiya Jumma’a 8 ga watan Satumba, al’ummar kasar Japan sama da dari sun gabatar da kara ga wata kotun dake yankin Fukushima na kasar Japan, inda suka zargi gwamnatin kasar gami da kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo wato Tokyo Electric Power Company a turance, da aikata laifin zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku ba bisa doka ba, tare da bukatar kotun da ta yanke musu hukuncin dakatar da wannan danyen aiki, abun da ya kasance kara ta farko da aka gabatar dangane da bukatar dakatar da zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku a kasar Japan, kana, kokari ne na daban da jama’ar kasar suka yi na kare hakkokinsu bisa doka, bayan da wasu kungiyoyin al’umma suka gabatar da kara kan firaministan kasar, Fumio Kishida.

Takardar kai karar ta ce, kafin ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, gwamnatin Japan ba ta taba gudanar da bincike a fannonin gurbata muhalli ko illoli ga muhallin halittu ba, kana, kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo na iya kara kafa manyan tankunan ajiye ruwan dagwalon nukiliyar maimakon zubarwa a cikin teku. Don haka, al’ummar Japan na ganin cewa, gwamnatin kasar gami da kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo sun aikata laifin gurbata muhalli, da keta hakkokinsu a fannin kamun kifi da tafiyar da rayuwa cikin kwanciyar hankali, abu ne da ya keta doka.

Zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku da gwamnatin kasar Japan take yi, babbar kasada ce da ba a taba ganin irinta ba a tarihi, wanda ke da alakar kut da kut da tsabtar muhallin yankunan teku a duniya, da lafiyar dan Adam gami da muradun zuriyoyinmu dake tafe. Kai karar gwamnati da al’ummar Japan suka yi, ya shaida babbar damuwa daga bangarori daban-daban gami da Allah wadai da suka yi. Kwararru na ganin cewa, abun da wadannan mutanen Japan suka yi, zai iya kara karfafa gwiwar sauran mutane don su kiyaye hakkokinsu bisa doka ta hanyoyi daban-daban. (Murtala Zhang)