logo

HAUSA

Dan wasan tseren Uganda Joshua Cheptegei ya lashe gudun mita 10,000 a karo na 3 a jere

2023-09-08 10:43:20 CRI

 

Dan wasan tseren kasar Uganda Joshua Cheptegei, ya lashe gudun mita 10,000 a karo na 3 a jere, bayan da ya kai ga samun wannan nasara a wasan karshe da aka fafata, yayin gasar wasannin motsa jiki ta duniya ta 2023 da aka kammala a kasar Hungary.

Joshua Cheptegei, ya kammala gudun sa ne a wannan karo, cikin mintuna 27 da dakika 51.42, inda aka bayyana shi a matsayin zakaran tseren maza na mita 10,000 ya kuma karbi lambar zinari ta gasar.

Cheptegei, mai shekaru 26 da haihuwa, ya yunkura, tare da wucewa gaba ne a tseren, lokacin da ake daf da kammalawa, duk da saurin sa a gasar ta bana, bai kai wanda ya taba kaiwa ba a baya, inda ya taba kaiwa karshen gudun na mita 10,000 cikin mintuna 26 da dakika 11.

A dai wannan karo, dan tseren kasar Kenya Daniel Simiu Ebenso, ya kasance na biyu, inda ya lashe lambar azurfa bayan kammala gudun sa cikin mintuna 27 da dakika 52.60, yayin da dan tseren Habasha Solemn Brega ya zo na 3, inda ya lashe lambar tagulla bayan kammala tseren sa dakika 0.12 bayan dan tseren Kenya.

Da yake tsokaci game da sanarar sa, Cheptegei ya ce "Na yi matukar farin ciki da alfahari, ganin yadda na lashe wannan kambi nawa a karo na 3 a jere. Wannan ne yanayi mafi kyau na karkare kakar wasannin bana. Wata kila wannan ya zama karon karshe da zan shiga gasar kasa da kasa, don haka lashe lambar zinari a wannan lokaci na da kima ta musamman."

A bangaren tseren mita 100 ajin maza kuwa, mai rike da kambin Fred Kerley bai kai ga nasara a wannan karo ba, inda ya fita daga gasar tun wasan kusa da kusan na karshe. Sakamakon haka, dan wasan tseren Amurka Noah Lyles ya karbe kambin a bana, inda a wannan karo ya kammala tseren sa cikin mintuna 9 da dakika 83.

Game da nasarar sa a wannan karo, Noah Lyles ya ce, "Na zo nan domin lashe zinari 3, na samu lashe na farko saura guda 2. Ina fatan lashe gudun mita 200 a Budapest. Ina ganin tseren mita 100 ya fi wahala. Ina fatan jin dadin dukkanin fafatawar da zan shiga. Ina cikin nishadi"

A wannan rukuni, dan tseren Botswana mai wasa a ajin ‘yan kasa da shekaru 20, wanda kuma ya lashe gasar duniya karo 2, Letsile Tebogo, a wannan karo ya lashe lambar azurfa, inda ya kafa sabon matsayin bajimta, bayan kammala gudun sa cikin mintuna 9 da dakika 88. Sai kuma dan tseren Birtaniya Zharnel Hughes, wanda ya biye masa baya da lambar tagulla.

A daya hannun kuma, dan tseren Italiya, wanda ya taba lashe lambar zinari ta gasar Olympic Lamont Marcell Jacobs, duk da ya kammala tsere cikin mintuna 10 da dakika 05, bai kai ga shiga wasan karshe a wannan karo ba.

Rahotanni sun nuna yadda Bence Halasz, dan kasar Hungary ya nuna bajimta, a yayin gasar jefa mummulallen karfe, inda ya jefa karfen sa ya wuce mita 80 kadan a jifan sa na farko. Bayan nan ne kuma takwaransa na Canada, wanda sabon-shiga ne a manyan gasanni Ethan Katzberg, ya yi nasarar jefa karfen sa zuwa nisan mita 81.25 a jifan sa na 5. Kaza lika dan wasan Poland Wojciech Nowicki ma ya yi jifan da ya kai mita 81.02.

Daga karshe dai a wannan karo, Halasz ya kasance a matsayi na 3, da nisan jifan mita 80.82, matakin da ya ba shi damar lashe lambar tagulla karo na 2 a gasar kasa da kasa.

A gasar heptathlon, mai kunshe da tsere, da tsallake shingaye, da sauran wasu wasannnin motsa jiki da ake yi a hade, ‘yar wasar Birtaniya Katarina Johnson-Thompson, ta sake lashe kambin da ya kubuce mata, inda a bana ta samu jimillar maki 6740.

A wasan tsalle mai nisa kuwa, ‘yar wasan Serbia Ivana Vuleta, ta lashe lambar zinari a ajin mata, inda a wannan karo ta yi tsalle zuwa nisan 7.14, wanda shi ne mafi nisa da aka samu a gasar ta bana.