logo

HAUSA

Li Qiang ya gana da shugaban kasar Indonesiya

2023-09-08 15:46:26 CMG HAUSA

 

Yau Jumma’a da safe, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo a Jakarta, babban birnin kasar.

Li Qiang ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana son ci gaba da zurfafa amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da kasar Indonesiya, da kara nuna goyon baya ga juna kan batutuwan da suka shafi muhimman moriyar juna da manyan batutuwan dake jawo hankalin juna. Bunkasa hadin gwiwa a fannoni daban-daban, da ci gaba da ciyar da ruhun Bandung gaba, da tabbatar da hadin kai na zahiri.

A nasa bangare shugaba Joko Widodo ya ce, kasarsa na nacewa ga manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kuma tana son karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin cinikayya da zuba jari, da aikin gona, da kamun kifi, da samar da ababen more rayuwa, da sabbin makamashi, ta yadda za a sa kaimi ga inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Yayin ziyarar Li Qiang a kasar, bangarorin biyu sun sa hannu kan takardun hadin gwiwa a fannoni daban-daban, ciki hadda masana’antu da aikin gona da kamun kifi da ciniki na yanar gizo da kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha. (Amina Xu)