logo

HAUSA

Masani: Yunkurin Sin na yakar kwararowar hamada abin koyi ne ga Afirka

2023-09-08 10:16:54 CMG Hausa

Wani kwararre a fannin muhalli dan kasar Masar, Magdy Allam ya bayyana cewa, kasar Sin ta shafe shekaru da dama tana kokarin kawar da hamada, kuma a halin yanzu ta zama babbar kafa ta samar da bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba a duniya, kana abin koyi ga kasashen Afirka.

Allam, wanda har ila shi ne mai ba da shawara a cibiyar kula da muhalli ta duniya, kuma babban sakataren kungiyar masu kula da muhalli na kasashen Larabawa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Laraba cewa, mayar da hamada zuwa dazuzzuka wani abin zaburarwa ne ga kasashen Afirka dake yaki da lalacewar kasa.

A cewar masanin nasarar da kasar Sin ta samu wajen kula da matsalar yanayi kamar fari da zafin rana da kuma matakan da ta dauka na magance dumamar yanayi, wata muhimmiyar gudummawa ce ga aikin kiyaye muhallin duniya.

Alkalumman hukuma sun nuna cewa, a tsakanin shekarar 2012 zuwa ta 2022, yawan gandayen daji na kasar Sin ya kai murabba'in eka miliyan 64, yayin da aka inganta eka miliyan 11 na filayen ciyawa, kana an kara ko maido da fiye da eka dubu 800 na filayen dazuka. (Ibrahim Yaya)