logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Jigawa ta gina ganuwa mai tsawon kilomita 100 a yakunan da suke fuskantar matsalar ambaliyar ruwa

2023-09-07 09:23:15 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Jigawa dake arewacin Najeriya ta samu  nasarar gina ganuwa mai tsawon kilomita 100 a yankunan da suke matukar fuskantar matsalolin ambaliyar ruwa a duk shekara.

Gwamnan jihar Malam Umar Namadi ne ya tabbatar da hakan jiya Laraba 6 ga wata, yayin wani taron manema labarai a birnin Dutse. Ya ce ganuwar za ta taimaka wajen dakile ruwan da yake ambaliya daga tafkunan  jihar zuwa cikin garuruwa da gonakai.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Gwamnan na jihar Jigawa wanda yake bikin cikarsa kwanaki 100 a kan mulki, ya ce, tun lokacin da ya kasance gwamnan jihar, ya mayar da hankalinsa sosai wajen ganin ya bullo da matakai da za su rage asarar dukiyoyi da kaddarori da al’ummar jihar ke yi a lokacin damuna sakamakon ambaliyar ruwa da kuma ballewar koguna.

Malam Umar Namadi ya ci gaba da cewa batun sha’anin noma na daya daga cikin burika 12 da gwamnatinsa ke son cimmawa kafin karewar wa’adin mulkinsa, kasancewa jihar Jigawa na daya daga cikin jihohin tarayyar Najeriya da take samar da abinci a kasa da kuma kasashe makwafta.

“Jihar Jigawa jihar noma ce mun yi ta kokarinmu ga yadda za mu yi mu saukakawa mutane harkar noman nan, ya zama daga abun da muka koye shi na gargajiya ana yi da fartanya da sauransu, domin inganta harkarta yadda zai kara adadin albarkar da ake samu bayan girbi, wanda gwamnatin da ta gabata ta yi nata kokarin wanda har aka kai ga nasarar bunkasa noman shinkafa, to wannan karon mun sayi tantan guda 54 ko da yake mun bayar da umarnin a kara zuwa 60. Dabararmu a nan shi ne za mu hada gwiwa da kananan hukumomi kowacce karamar hukuma za mu ba ta tan-tan guda biyu. Haka kuma mun sa a kawo injuna masu amfani da hasken rana, wanda za mu rabawa manoma shima a wani farashi mai rahusa domin su samu su yi ban ruwa da shi kuma muna ganin idan aka yi hakan noman zai yi masu riba in Allah ya yarda.”

Haka gwamnan ya ce, a yanzu haka akwai kamfanoni sama da 50 da suka nuna sha’awar saka jarinsu a bangaren noma da hakar ma’adanai a jihar wanda a halin da ake ciki, 19 daga cikin irin wadannan kamfanonin sun iso jihar. (Garba Abdullahi Bagwai)