logo

HAUSA

‘Yan wasan wushu na Afghan na shirin fafatawa a gasar wasannin nahiyar Asiya dake tafe a Hangzhou

2023-09-07 21:30:37 CMG Hausa

Yayin da lokacin gudanar da gasar wasannin nahiyar Asiya da za a gudanar a birnin Hangzhou na kasar Sin ke karatowa, a wani dakin horas da ‘yan wasan motsa jiki dake birnin Kabul na kasar Afghanistan, ‘yan wasa 6 dake wasa cikin rukunin mutum biyu biyu, na ta kokarin samun horo, duk da karancin kayan wasa da suke fuskanta, da kuma tsananin zafi da ake yi. ‘Yan wasan na wushu wato wasan fada salon Kung Fu, na fatan shiga a dama da su a gasar ta nahiyar Asiya karo na 19, wadda za a bude a ranar 23 ga watan Satumban nan.

A cewar mahukuntan kungiyar ‘yan wasan wushu ta Afghanistan, ‘yan wasan kasar 4 ne za su wakilci kasar, sai kuma koci da jagoran kungiyar, inda za su shiga gasar wushu Sanda ta nuna fasahar fada, da sauran dabarun zamani na fada da aka kara cikin wasan.

Hukumar dake lura da wasan na wushu a Afghanistan ce ta zabo ‘yan wasa mafiya kwarewa, domin su wakilci kasar a gasar ta Hangzhou dake tafe. An dai kafa wannan hukuma ta “Afghanistan wushu Federation” ne a lardin Herat na yammacin kasar a shekara ta 2000.

Babban kocin wushu na kasar Gulgul Shah Khalid, ya ce hukumar ta yi rajistar sama da ‘yan wasan wushu 6,000 daga lardunan kasar 28. Wadannan ‘yan wasa na shiga gasannin wushu Sanda, na nuna dabarun fada, da kuma salon Taolu mai kunshe da raye-raye da nuna fasahohin wasan.

Khalid ya ce "Muna da ‘yan wasa 44 dake yin atisaye a kullum karkashin kulawar hukumar kasar mu".

Mohammad Khalid Hotak, matashi ne mai shekaru 30, kuma daya ne daga cikin ‘yan wasa wushu mafiya kwarewa a Afghanistan. Hotak ya ce wasan wushu ya fara burge shi tun yana karami, lokacin da ya ke kallon fina-finan kwararrun taurarin wasan na kasar Sin, irin su Jackie Chan da Jet Li. Don haka a yanzu da zai ziyarci kasar Sin domin shiga babbar gasa, wani mafarki ne da ya jima yana fatan ya zama gaskiya.

Ya ce "wushu na kunshe da sakon da’a, da zaman lafiya, da kauna da abota, yana kuma haifar da zaman jituwa da ‘yan uwantaka"

A shekarar 2013, Hotak ya yi nasarar lashe lambar Tagulla a gasar wushu ajin maza masu nauyin kilogiran 60 salon Sanda. A lokacin gasar ta kasa da kasa karo na 12, ta gudana ne a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia. Kuma wannan ne karo na farko da Hotak ya yi nasarar lashe lambar yabo a wasan wushu a matakin gasar kasa da kasa.

A cewar Hotak, "Na fafata da ‘yan wasan kasar Sin har sau 4. Yanayi ne mai ban sha’awa, ya kuma ba ni damar fahimtar salon wasan Sinawa. A wannan karo zan shiga gasar wushu ajin maza masu nauyin kilogiram 70 a gasar ta birnin Hangzhou. Wasan wushu bai shahara ba sosai a Afghanistan, kuma ‘yan wasan wushu ba sa samun albashin wata wata kamar ‘yan wasan kasa dake buga kwallon kafa ko cricket. Don haka ta hanyar shiga gasannin kasa da kasa, da lashe lambobin yabo ne kadai muke iya cin ribar wannan sana’a ta mu. Mu 11 ne a gidan mu, mahaifi na ya bani goyon baya kwarai, ina farin cikin ci gaba da yin wannan wasa, ko shakka ba bu iyali na sun bani goyon baya. Don haka zan ci gaba da kokari matuka, wajen lashe gasannin kasa da kasa, kuma ina da burin kara gabatarwa, da yayata wasan wushu ga al’ummar Afghanistan ta hanyar harkoki na na rayuwar yau da kullum”.

Da yake tsokaci game da shirin Afghanistan na shiga gasar Hangzhou dake tafe, shugaban tawagar ‘yan wasan Wushu da za su halarci gasar Ehsan Ahmed Karukhil, ya ce ‘yan wasa mafiya hazaka ne kadai suka samu shiga tawagar da za ta fafata a Hangzhou. An dauki tsauraran matakan tace ‘yan wasan, inda aka zabo ‘yan wasa irin su Hotak.

Da fari dai hukumar ta wushu na zabar wakilai ‘yan wasan daga lardunan kasar ne, sannan sai a gudanar da gasar kasa baki daya, inda ake zabar mambobin tawagar kasar su 4. Idan ba a bukatar ‘yan wasa 4 a gasar da za a shiga, sai a sake tantance mafiya kwarewa domin zabar mafiya cancanta.

Karukhil ya shafe kusan shekaru 28 yana koyar da wasan wushu. A shekarar 2008, ya zama alkalin wasan kasa da kasa a fannin. Ya kuma ga kalubaloli da nasarorin da wasan ya samu a Afghanistan cikin waadannan shekaru.

A cewar sa, yaki da kasar ta fuskanta ya sanya ‘yan wasan motsa jiki da dama barin kasar, amma duk da haka akwai mutane masu yawa dake nacewa yin atisaye iya iyawar su. Kaza lika rashin isassun kudade na sayan kayayyakin da ake bukata yayin wasan wushu salon Taolu, ya sa dole ‘yan wasan kasar ke shiga nau’in wasan na wushu na Sanda kadai.

A cewar kocin, mafiya yawa na ‘yan wasan na fitowa ne daga iyalan yankuna marasa galihu, kuma da yawa daga cikinsu sai sun yi kananan ayyuka, kafin da kuma bayan atisayen su, saboda su saukakawa iyalan su bukatun rayuwa.

Karukhil ya ce "Alal hakika, wannan gasa dake tafe babbar gasa ce. Kuma a baya Afghanistan ta taba lashe lambar yabo a makamanciyar ta, don haka muna da fatan cimma karin nasarori, da sakamako mai kyau a gasar ta bana".

A cewar hukumar lura da harkokin motsa jiki, karkashin ma’aikatar wasanni da motsa jiki ta kasar, tawagar kasar za ta fafata a gasar bana ta Hangzhou, a nau’o’in wasanni 17, ciki har da wasan wushu, da kwallon kafa, da volleyball da cricket da sauran su.