logo

HAUSA

Rashin ingantattun titunan mota na baiwa ’yan ta’adda damar kai hare-hare cikin sauki a jihar Niger

2023-09-06 09:13:52 CMG HAUSA

 

Gwamnatin jihar Niger ta Najeriya ta tabbatar da cewa, rashin ingantattun tinunan mota na daya daga cikin damar da ’yan ta’adda ke amfani da shi wajen kai hare-hare a sassa daban daban na jihar.

Gwamnan jihar Alhaji Muhammad Umar Bako ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake ganawa da shugabanin al’umomi da ’yan siyasa a gidan gwamnatin jihar dake Mina.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.