logo

HAUSA

Kasar Sin na kokarin yin hadin gwiwar sauran kasashen duniya wajen neman farfadowar tattalin arzikin kasa da kasa tare

2023-09-06 08:43:50 CGTN Hausa

A yayin da duniya ke dada dunkulewa waje guda, bukatun kasashen duniya mabanbanta na kara cudanya da juna yayin da shugabannin kasashe ke musayar ra’ayi dangane da yadda za ayi mu’amala don samun moriyar juna da farfadowar tattalin arziki. 

A bisa wannan dalilin ne “kasar Sin ke kokarin hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya wajen neman farfadowar tattalin arzikin duniya. Masana daga kasashen waje sun yi tsokaci kan jawabin shugaba Xi Jinping na bikin baje kolin cinikayyar hidimomi ko CIFTIS na shekarar 2023 da ke gudana anan birnin Beijing, inda ya bayyana  matsayin kasar Sin a fannin bude kofa da niyyarta ta ci gaban bunkasuwar duniya, abin da ya karawa duniya kwarin gwiwa da karfin tinkarar kalubalen tattalin arziki  da samun ci gaba mai wadata da dorewa.

Domin bunkasa damar ci gaba a fannin kara bude kofofin kasar Sin, ta yadda kowa zai iya shiga a dama da shi, Sin ta fadada damammakin kasa da kasa na inganta yankunan cinikayya maras shinge, tana kuma shiga ana damawa da ita wajen gudanar da shawarwari kan ci gaban cinikayyar hidimomi da na zuba jari.  

Kasar Sin ta gudanar da wasu ayyuka fiye da dari na samar da makamashi mai tsabta, da samun ci gaban tattalin arziki tare da kare muhalli a lokaci guda, cikin wadannan ayyukana akwai yankin rage hayaki mai dumama yanayi, da yankin tinkarar sauyin yanayi a nahiyar Afirka, da taimakawa kasashen Afirka gina “shingen kare kwararowar hamada”. A Najeriya, akwai tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Zungeru da dai makamatansu. (Muhammad Baba Yahaya, Saminu Alhassan, Sanusi Chen)