logo

HAUSA

Ramaphosa: Afirka ta Kudu ta amfana matuka daga BRICS

2023-09-06 15:13:58 CGTN HAUSA

 

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa, kasarsa ta samu gagaruman alfanu daga kungiyar BRICS.

Shugaban ya bayyana hakan ne a yammacin jiya, a yayin wani taron amsa tambayoyi da aka gudanar a majalisar dokokin kasar dake birnin Cape Town, babban birnin majalisar dokokin kasar.

Ramaphosa ya shaidawa ’yan majalisar cewa, Afirka ta kudu ta samu gagarumar fa'ida ta hanyar kasancewarta mamba da kuma alakarta da kungiyar kasashen BRICS.

Ya bayyana cewa, zama mambar kungiyar BRICS ya taimaka wa kasarsa wajen habaka zuba jari, da harkokin kasuwanci, da fannin yawon bude ido, da koyon sana'o'i da kara karfin fasaha. (Ibrahim Yaya)