logo

HAUSA

An kaddamar da taron MDD karo na 78

2023-09-06 10:34:47 CGTN HAUSA

 

A jiya Talata ne aka bude babban taron MDD karo 78, karkashin jagorancin sabon shugaban zaman Dennis Francis. Cikin sakonsa na bude taron, babban magatakardar MDDr Antonio Guterres, wanda mataimakiyarsa Amina Mohammed ta karanta, ya yi gargadi game da kalubaloli masu zurfi, da rarrabuwar kawuna dake addabar MDD.

A nasa bangare kuwa, shugaban taron Dennis Francis, cewa ya yi sabon zaman da aka bude a wannan karo, na zuwa ne a gabar da muhimman bukatun duniya ke fuskantar jerin kalubaloli masu wuyar sha’ani. Francis ya ce akwai bukatar kasashe mambobin majalissar, su yi hadin gwiwar ingiza matakan wanzar da zaman lafiya, ta hanyar karfafar masu rauni, ta yadda za a kai ga rarraba nasarori daga albarkatun dake haifar da manyan sakamako.

Kazalika, Francis ya yi fatan ganin an ingiza cimma nasarori, bisa fifikon kwazon matasa, da kirkire-kirkire, da fasahohi, da wanzar da bunkasuwa.    (Saminu Alhassan)