logo

HAUSA

Firaministan Sin ya halarci liyafa tare da 'yan kasuwan Sin da Indonesia

2023-09-06 11:20:04 CGTN Hausa

A jiya Talata, firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci wani bikin liyafa tare da 'yan kasuwa, da masu masana'antu na kasashen Sin da Indonesia, a birnin Jakarta na kasar Indonesia. A cikin mahalarta liyafar har da Luhut Pandjaitan, ministan kasar Indonesia mai kula da teku da zuba jari, kuma babban jami’in kasar mai kula da aikin hadin gwiwa da kasar Sin, gami da wasu manyan 'yan kasuwa, da masu masana'antu na kasashen Sin da Indonesia kimanin 200.

Mista Li ya yi jawabi a wajen bikin liyafar, inda ya ce huldar dake tsakanin kasashen Indonesia da Sin na ta samun ci gaba a cikin shekarun nan, a karkashin jagorancin shugabannin kasashen 2, inda wannan yanayi mai armashi ya zama abin misali ga sauran kasashe makwabta.

Ya ce, kasar Sin na son habaka hadin kanta da kasar Indonesia, musamman ma a fannonin makamashi mai tsabta, da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani. Kana ya bayyana fatansa na ganin 'yan kasuwa, da masu masana’antu na kasashen 2 sun ba da gudummowa ga yunkurin zurfafa zumunta, da inganta hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2, gami da samun damar raya harkokinsu a lokaci guda. (Bello Wang)