Tawagar ’yan wasan Wushu ta Afghanistan ta shirya halartar wasannin Asiya a Hangzhou
2023-09-05 10:11:05 CMG Hausa
Rahotanni daga kasar Afghanistan na cewa, yanzu haka ’yan wasan fasahar Wushu na kasar guda 6, suna fafatawa da juna a wani dakin atisaye dake birnin Kabul, inda suke motsa jiki da kayayyaki kalilan, a daidai lokacin da ’yan wasan ke shirye-shiryen halartar gasar wasannin Asiya karo na 19 da za a bude ranar 23 ga watan Satumba a birnin Hangzhou na kasar Sin.
A cewar hukumar kula da wasan fasahar gargajiya ta Wushu ta kasar Afganistan, hukumar za ta tura 'yan wasa hudu da koci da kuma shugaban kungiyar da za ta fafata a gasar Wushu Sanda, wasan fasaha mai kama da wasan gargajiya na Kung-Fu gami da dabarun kare kai na zamani.
An kafa hukumar wasan Wushu ta Afghanistan wadda aka dora mata alhakin zabar fitattun ’yan wasa a tawagar kasar ce a lardin Herat dake yammacin kasar a shekara ta 2000.
A jawabinsa, jami’in horas da ’yan wasan, Gulgul Shah Khalid ya ce hukumar ta yi rijistar ’yan wasan Wushu sama da dubu 6 daga larduna 28 na kasar. Kuma yanzu haka sun tsunduma cikin kara kwarewa a fasahohin wasan Wushu Sanda, da kuma Taolu, wanda ke nufin tsarin motsa jiki na wasan.
Bisa jerin sunayen da ofishin koyar da wasannin motsa jiki na babban daraktan kula da harkokin motsa jiki da wasanni na Afghanistan ya nuna, kungiyoyin wasanni 17 da suka hada da Wushu, da kwallon kafa, da kwallon raga da wasan kurket ne, za su halarci gasar wasannin Asiya ta Hangzhou. (Ibrahim Yaya)