logo

HAUSA

Jami’an tsaro sun ceto mutane 16 daga masu garkuwa da mutane a arewa maso gabashin Najeriya

2023-09-05 10:39:30 CMG Hausa

A kalla mutane 16 ne gamayyar jami’an tsaron Najeriya suka ceto, daga wani gungu na masu garkuwa da mutane, sakamakon wani samame a yankunan kananan hukumomin Ningi da Toro dake jihar Bauchi, a arewa maso gabashin kasar.

Da yake karin haske kan hakan cikin wata sanarwa, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Bauchi Ahmed Wakili, ya ce hadakar jami’an soji, da ‘yan sanda, da wasu ‘yan sa kai ne suka gudanar da samamen a ranar Asabar, bayan samun bayanan sirri.

Wakili ya ce cikin mutanen da aka ceto, 5 sun jikkata, yayin da 11 ke cikin koshin lafiya. Kaza lika jami’in ya ce sun yi barin wuta, tare da tarwatsa gungun masu garkuwa da mutanen bayan sun ci lagon su.

Bugu da kari, ana ci gaba da matsa kaimin zakulo bata garin da suka tsere, wasun su dauke da harbin bindiga, domin gurfanar da su gaban kuliya.    (Saminu Alhassan)