logo

HAUSA

Jerin gwano da taron gangami kusa da sansanin sojojin Faransa dake Yamai domin bukatarsu da su fice

2023-09-05 09:17:57 CMG Hausa

A ranar Asabar 2 ga watan satumban shekarar 2023, ’yan Nijar sun sake fitowa domin bukatar sojojin Faransa da jakadan kasar Faransa dake Nijar da su fice daga kasar. Dubban mutane ne suka amsa kiran kungiyoyin fararen hula a nan mahadar « Rond-Point Escadrille » dake kusa da sansanin sojojin Faransa.

Ga rahoton da abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana daga birnin Yamai bayan ya samu wutar lantarki a ofishinsa.