Huawei ta kaddamar da sabuwar wayar salularta ta Mate60
2023-09-05 09:25:46 CMG Hausa
Kwanan baya, kamfanin Huawei ya kaddamar da sabuwar wayar salularta samfurin Mate60 ba zato ba tsammani, lamarin da ya haddasa muhawara tsakanin sassa daban daban na kasar Sin, kana kasashen duniya sun mai da hankali sosai kansa. Bari mu kara sani kan matattarar bayanai ta microchip Kirar 9000s da ke cikin wannan sabuwar wayar salula, wadda kasar Sin ta kera da kanta, duk da takunkumin da kasar Amurka take sanya mata. (Tasallah Yuan)