logo

HAUSA

Manyan nasarorin da CMG ya samu yayin hadin gwiwar da ya yi da kasashen nahiyar Afirka a fannin al’adu

2023-09-05 15:45:10 CMG Hausa

Bana ake cika shekaru 25 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Afirka ta Kudu a cikin wannan lokaci na musamman, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ya je kasar Afirka ta Kudu, inda ya gudanar da wasu ayyukan watsa labarai masu inganci kuma ya kawo wasu kyawawan shirye-shiryensa. Sun tattauna matakan karfafa hadin gwiwa, ta yadda suka sami babban sakamakon hadin gwiwa a fannoni daban daban, matakin da ya karfafa mu’amala da hadin gwiwa tsakanin al’adun Sin da na kasashen Afirka. A cikin shirinmu na yau, za mu ji irin manyan nasarorin da CMG ya samu yayin hadin gwiwar da ya yi da kasashen nahiyar Afirka a fannin al’adu.