logo

HAUSA

Firaministan rikon kwaryar Nijar ya gana da jakadan kasar Sin a Nijar mista Jiang Feng

2023-09-05 13:51:34 CMG Hausa

Firaministan rikon kwarya na Jamhuriyar Nijar Mahamane Ali Lamine Zeine ya gana da jakadan kasar Sin a Nijar mista Jiang Feng a fadar faraminista da ke birnin Yamai a jiya litinin 4 ga watan Augustan shekarar 2023.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da rahoto.

Ita dai wannan ganawa tsakanin manyan jami’an biyu na zuwa daidai da lokacin da kasar Nijar take kokarin neman bakin zaren makomarta a karkashin jagorancin sabbin hukumomi tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, ta nuna kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Mista Jiang Feng ya bayyana wa ‘yan jarida manufar wannan ganawa tare da shugaban gwamnatin rikon kwaryar Nijar.

“Wannan ganawa ta maida hankali musamman ma kan halin da kasar Nijar take ciki. Gwamnatin Sin na ba da muhimmanci sosai kan ci gaban halin da ake ciki a Nijar. Kasar Sin har kullum tana ci gaba da manufarta na kin tsoma bakinta cikin harkokin cikin gida na sauran kasashe, kuma tana bayyana goyon bayanta har kullum ga kasashen Afrika na su daidaita matsalolinsu a tsakaninsu. Haka zalika, gwamnatin kasar Sin tana son taka muhimmiyar rawa a matsayin mai shiga tsakani bisa girmama kasashen shiyyar domin cimma wata mafitar siyasa ga wannan rikici na kasar Nijar.”

Daga karshe, jakadan kasar Sin a Nijar mista Jiang Feng ya ce kasar Sin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da karfafa huldar dangantaka ta moriyar juna da kuma ciyar da ita gaba domin jin dadin al’umomin kasashen Sin da Nijar.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.