logo

HAUSA

An rantsar da Brice Oligui Nguema a matsayin “shugaban rikon kwarya” na Gabon

2023-09-04 20:08:06 CMG

A yau Litinin ne aka rantsar da Brice Oligui Nguema, shugaban kwamitin rikon kwarya da maido da ayyukan hukumomi a Gabon ko CTRI, a matsayin “shugaban rikon kwarya” na Gabon a birnin Libreville.

A ranar Larabar da ta gabata ne wasu gungun hafsoshin sojan kasar suka nada Nguema, babban kwamandan rundunar tsaron kasar Gabon, a matsayin shugaban rikon kwarya da sunan CTRI, biyo bayan juyin mulkin da suka yi da sanyin safiyar ranar, bayan da hukumar zaben kasar ta sanar cewa shugaba Ali Bongo Ondimba ya sake lashe zabe a matsayin shugaban kasar. (Yahaya)