logo

HAUSA

Masani: Wajibi ne Amurka ta amince da karuwar tasiri da ma karfin kasar Sin

2023-09-04 15:26:17 CMG Hausa

Wata makala da Yasar Bukan, malami a harkokin siyasar kasa da kasa kuma falsafar siyasa a jami’ar Metropolitan dake birnin Toronton Canada ya wallafa a kafar watsa labaran Amurka mai suna UPI, ta bayyana cewa, da alama kasar Sin za ta yi nasara a kokarin da take yi, kuma a karshe Sin da Amurka za su koyi zama tare da samun bunkasuwa.

Amurka ba ta nuna sha'awar raba jagorancin duniya, haka nan kasar Sin ba ta nuna sha'awar kauce wa burinta a fagen kasa da kasa ba, duk da cewa suna iya yin karo da juna.

Ya kuma kara da cewa, Amurka ba ta yi nasarar dakile ci gaban kasar Sin ba, kuma mai yiwuwa ba za ta iya hana kasa mai karfin tattalin arziki ta biyu cimma burinta na shekaru dari ba. Ya kara da cewa, kasar Sin ta zuba jari a sassan fadin duniya, ta samar da kayayyaki, kuma ra'ayin jama'a a sassan duniya game da kasar Sin yana sauyawa.

Sharhin ya ce, kasar Sin wata cibiya ce mai tarin damammaki kuma tana da karfi da kudirin iya kirkiro abubuwa da dama. Cibiyar tana da haɗin kai da inganci. Misali, lokacin da aka hana kasar Sin shiga tashar binciken sararin samaniyar kasa da kasa bayan amincewa da wata doka da majalisar dokokin Amurka ta yi a shekarar 2011, Sin ta gina tashar Tiangong, tashar binciken sararin samaniya ta din-din-din mallakinta. (Ibrahim)