logo

HAUSA

Yaushe Japan Za Ta Kawo Karshen Laifinta?

2023-09-04 11:21:24 CMG HAUSA

DAGA MINA

Kwanan baya, a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ministan kula da aikin gona da dazuzzuka da aikin su na kasar Japan Nomura Tetsuro ya bayyana ruwan da gwamnatin kasar ta zubar a cikin teku a matsayin ruwa dagwalon nukiliya, lamarin da ya sa firaministan kasar Fumio Kishida fushi sosai, saboda hakan ya sa matakan da gwamnatin ta dauka na boye laifinta sun zama banza.

Amma, mene ne ra’ayin bangarori daban-daban game da matakin da gwamnatin Japan ta dauka na zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku? Ran 1 ga wata, wata kungiya mai zaman kanta ta al’ummar Japanawa da ake kira “kungiyar tuntubar juna kan yaki da zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku”, ta kai karar firaministan kasar Fumio Kishida da shugaban kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo, don nuna rashin jin dadinsu game da matakin zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku da jami’an suka amince a yi, ba tare da yin la’akari da ra’ayin jama’a ba. Kungiyar ta ce, ruwan da aka sarrafa na kunshe da sinadarai masu guba, wadanda aka kasa cire su. Kuma matakin da gwamnatin ta dauka na cike da kuskure. 

Sai kuma Amurka wadda ta yi shelar goyon bayan matakin da Japan ta dauka, a hakika, tuni ta dauki matakai na kayyade shigo da kayayyakin gona da na teku daga Japan, musamman ma abinci daga wurin da guba suka fi bazuwa.

Duk wadannan abubuwa na shaida cewa, ruwan da Japan ta zuba cikin teku ruwan dagwalon nukiliya ne wanda ke barazana ga lafiyar ‘yan Adam da halittun teku. Don haka, dole ne Japan ta dakatar da laifinta, kuma ta dauki matakin da ya dace. (Mai zane da rubutu: MINA)