logo

HAUSA

Al’adun Iyali da aka gada daga kaka da kakani

2023-09-04 19:33:18 CMG Hausa

Tun shekaru fiye da dubu biyu da suka wuce, mai hikima Confucius na kasar Sin a cancancan da ya ba da fifiko kan koyon ilmi, har ma ya zama abin koyi wanda ya cancanci a koya har abada. Ra’ayin da Confucius ya assasa, da akidun da ya bunkasa bisa wannan tunani, sun yi tasiri sosai ga wayewar kan kasar Sin.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna cewa, “An haife mu a matsayin Sinawa, kuma muhimmin abu shi ne, muna da ruhin musamman na al'ummar Sinawa, da kuma dabi'un da jama’ar kasar ke amfani da su a yau da kullum da ba su sani ba. Muhimman dabi'un gurguzu da muke dabbakawa sun hada da gado da kuma daukaka kyawawan al'adun gargajiya na kasar Sin.”

Confucius ya ce, “Idan mutane ba su da imani, ba su san abin da za su yi ba.” Mutunci shi ne ginshikin daidaita rayuwar dan-Adam da gudanar da kasar.

Al’amura sun canza, amma al’adun iyali ba su canja ba, a cikin Ka’idoji da Dokoki na Iyalin Confucius an rubuta cewa, “Ya kamata a koya wa zuriyar dake tafe ka’idoji da dokoki da aka gada daga kaka da kakanni, kuma a tabbata sun karanta tare da fahimtarsu bil hakki da gaskiya.”

Dukkan manyan sauye-sauye da suka faru a zamani ko a yanayin rayuwarmu, dole ne mu mai da hankali wajen gina iyali, wanda ya hada da ilimin iyali, da kuma tarbiyar iyali. Kong Minghui, malamin ilimin siyasa da tarbiya na Chongguangmen dake gidan Confucius, ya bayyana wa daliban dalla-dalla yanayin iyali da ilimin iyali na Confucius. 

“Ci gaban kowa ce kasa ko al'umma yana tafiya dogara ga ci gaban al'adunta a ko da yaushe, kuma cimma babban burin farfado da al’ummar Sinawa na dogaro da ci gaban al'adun kasar.” A watan Nuwamban shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci Gidan Confucius da Kwalejin Nazarin Confucius dake birnin Qufu na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin, domin kara fahimtar yadda ake jagorantar aikin gado da raya kyawawan al'adun gargajiya na kasar Sin.

A watan Satumba na shekarar 2014, a yayin bikin bude taron tattaunawa na kasa da kasa na tunawa da cika shekaru 2565 da haihuwar Confucius, da kuma babban taro na biyar na kungiyar akidun Confucius ta kasa da kasa, Xi Jinping ya nakalto layin farko na Tsararren Kundin Kalmomi da Akidun Confucius dake cewa, "Abin farin ciki ne samun abokai daga nesa", don maraba da mahalarta taron daga kasashe daban daban.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, akidun Confucius, da sauran akidu da al'adu da aka samar a lokacin kafuwar al'ummar kasar Sin, da ci gaban al'ummar kasar, sun zayyana yadda Sinawa ke gudanar da ayyuka a fannin ruhi, da tunaninsu da hankali, da nasarorin da suka cimma a fannin al'adu a fafutukar gina kasarsu tun zamanin da. Hakan na nuni da yadda al'ummar kasar Sin ke amfani da ruhi, kuma muhimmin abu ga al'ummar kasar wajen samun bunkasuwa.

Bisa la'akari da umurnin shugaban kasar, tsohon birnin Qufu ya kebe wuraren "Tsohon Confucius uku" wato Gidan Confucius, da Gidan Ibada na Confucius, da kuma Kaburburan Confucius da Iyalansa a matsayin mafari, kuma ya kara da "Sabbin wuraren Confucius Uku" da suka hada da Kwalejin Nazarin Confucius, Gidan Tarihi na Confucius, da Nishan Mai Tsarki wato wurin da aka haifi Confucius, don inganta al'adun kasar Sin, da kara ilimantar da jama’a game da wannan falsafa a sabon zamani.

A lokacin bazara, birnin Qufu dake lardin Shandong yana jan hankalin masu yawon bude ido da yawa, Gidan Confucius, da Gidan Ibada na Confucius, da Kaburburan Confucius da Iyalansa masu kyau da haskakawa, sun kwashe dubban shekaru suna yada al’adun gargajiya na Confucius.

Tsohon rukunin gine-gine na Gidan Ibada na Confucius, wanda ke tsakiyar birnin Qufu daga arewa zuwa kudu, yana da ma'auni mai girma da tsayayyen tsari.

Daga bangaren gabashin Gidan Ibada na Confucius, akwai Gidan Confucius da aka sani da "Iyali na Farko a Duniya", wanda ya kunshi gine-ginen da aka yi da shudin tubali da tayin mai launin toka.

Kabarin Confucius yana arewacin birnin Qufu, akwai duwatsun da aka sassaka kalmomi a kansu da yawa, hanyar zuwa wajen kabarin Confucius ta tsawon fiye da mita dubu daya.

A shekarar 1994, Majalisar Dinkin Duniya ta sanya wuraren "Confucius Uku" wato Gidan Confucius, da Gidan Ibada na Confucius, da kuma Kaburburan Confucius da Iyalansa a cikin jerin abubuwan tarihi na duniya.

"Idan kuna son kara fahimtar kasar Sin, ya kamata ku fara fahimtar Confucius, idan kuna son kara fahimtar Confucius, dole ne ku ziyarci wuraren 'Confucius uku'." Yang Chaoming, tsohon shugaban Kwalejin Nazarin Confucius, kuma fitaccen farfesa na kwalejin nazarin akidun Confucius na jami'ar Shandong, ya bayyana cewa, al'adun da Confucius ya kafa, wani muhimmin bangare ne na al'adun gargajiyar kasar Sin. Akidar da Confucius ya gabatar ta "kauna, aminci, ladabi, hikima, da mutunci" har yanzu su ne ruhin al'ummar Sinawa.