logo

HAUSA

Majalisar dokokin Afrika ta Kudu za ta gudanar da bincike kan gobarar da ta auku a Johannesburg

2023-09-04 09:54:47 CMG Hausa

Majalisar dokokin kasar Afrika ta Kudu, ta ce za ta gudanar da bincike kan mummunar gobarar da ta auku a Johannesburg.

Gobarar da ta tashi a wani gini mai hawa 5 a tsakiyar birnin Johannersburg da sanyin safiyar Alhamis, ta yi sanadin mutuwar mutane 77, baya ga wasu gommai da suka jikkata.

Wata sanarwa da majalisar dokoki ta kasar ta fitar a ranar Asabar, ta ce shugabannin majalisar da suka hada da Nosiviwe Mapisa-Nqakula da Mr. Amos Masondo sun lashi takobin majalisar za ta nazarci yanayin biyo bayan gobarar ta Johannesburg da ta kai ga asarar rayuka da jikkatar mutane da dama, kana wasu sama da 300 sun rasa matsugunansu.

Sanarwar ta ce za a dorawa kwamitoci masu ruwa da tsaki alhakin bibiyar dukkan matakai na gajere da dogon zango da sassan gwamnati daban-daban ke gudanarwa dangane da aikin tunkarar iftila’i.

A cewar sanarwar, manufar aikin ita ce nazarin irin wadannan gine-gine da bata gari ke kwacewa suna bayar wa haya ba bisa doka ba, kamar wanda gobara ta aukawa a Johannesburg. (Fa’iza Mustapha)