logo

HAUSA

'Yan Koriya ta Kudu sun kara yin zanga-zangar nuna adawa da zubar da ruwan dagwalon nukiliyar Japan

2023-09-03 16:57:50 CMG

A jiya Asabar ne dubban mutanen Koriya ta Kudu da suka hada da masunta da ‘yan gwagwarmaya da kuma 'yan siyasa suka ci gaba da gudanar da zanga-zangar karshen mako a tsakiyar birnin Seoul, don nuna adawa da yadda Japan ta zuba ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku.

Mahalarta zanga zangar sun yi ta rera taken "a dakatar da zuba ruwan dagwalon nukiliya cikin teku" da kuma "a hana shigo da dukkan kayayyakin ruwa na kasar Japan," suna masu kira ga gwamnatin Koriya ta Kudu da ta shigar da kara a gaban kotun kasa da kasa bisa dokar teku kan gwamnatin Japan.

Bisa ga binciken da aka gudanar a tsakanin manya 1,000, kashi 72.4 cikin dari sun ce suna adawa da zubar da ruwan dagwalon nukiliyar na Japan cikin teku.

Kashi 78.3 cikin 100 na wadanda suka bayar da amsa ga binciken sun ce ya kamata Koriya ta Kudu ta hana shigo da duk wani nau'in abincin teku daga Japan, kuma kashi 67.4 cikin 100 sun amsa cewa ya kamata 'yan Koriya ta Kudu su kauracewa kayayyakin Japan.

Lee Seo-yoon, wata uwa mai ‘ya’ya uku, ta bayyana a yayin zanga zangar cewa, “Ruwan dagwalon nukilyar Fukushima kayan shara ce,” inda ta kara da cewa Japan na daukar teku a matsayin mafi girma kuma mafi arha jakar shara.

Kim Sam-ho, wani masunci da ya fito daga gundumar Wando da ke gabar tekun kudancin kasar ya ce "Teku shine makomar iyalina da kuma makomar zuriyarmu." Kim ya nuna shakku sosai game da rashin hadarin ruwan dagwalon, yana mai kira ga gwamnatin Koriya ta Kudu ta dauki matakan da suka dace ciki har da matakan tallafawa masunta. (Yahaya)