logo

HAUSA

Najeriya ta yi kira ga MDD da ta kara tallafawa kasar yaki da ta’addanci

2023-09-02 20:31:38 CMG Hausa

Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu, ya gana da mataimakin sakataren MDD mai kula da harkokin yaki da ta’addanci Vladimir Voronkov, a birnin Abuja fadar mulkin kasar, inda ya yi kira ga MDD da ta kara tallafawa kasar wajen yaki da ta’addanci.

Rahotannin da fadar shugaban kasar ta fitar a jiya Juma’a, sun ce Bola Tinubu ya soki akidun ta’addanci, a matsayin abubuwan da suka illata ci gaban kasar, da zaman lafiyar al’umma, yana mai fatan MDD za ta kara goyawa gwamnatin sa baya, kasancewar ba za a iya tabbatar da bunkasuwa da wadata ba, karkashin kalubalen ta’addanci.

A nasa bangare, Vladimir Voronkov, ya ce Najeriya ta taka rawar gani a fannin yaki da ta’addanci a duniya, kuma majalisar na shirin gudanar da taron koli na yaki da ta’addanci a watan Afrilun shekarar badi, inda za a mai da hankali kan wannan batu a Afrika. (Amina Xu)