logo

HAUSA

An bukaci sojojin Najeriya da su kaucewa sauraron irin labaran da ake yadawa a kafofin sada zumunta

2023-09-02 15:44:23 CMG Hausa

Babban hafan sojin Najeriya Lieutenant General Toareed Lagbaja ya hori sojojin kasar da su kaucewa amfani da irin labarun da suke yawo a kafofin sada zumunta wadanda ke ingiza halayyar cin amanar kasa kamar yadda yake faruwa a wasu kasashen Afrika.

Ya bukaci hakan ne jiya Juma’a 1 ga wata  lokacin da ya kai ziyara barikin sojoji na  Maimalari dake Maiduguri, inda ya gana kai tsaye da dakarun musamman dake yaki da ayyukan ’yan kungiyar Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Lietunenant General Toareed Lagbaja ya bukaci sojojin dake fagen fama da su kara mayar da hankali wajen shawo kan  kalubalen dake gabansu a wannan shiyya

Domin baiwa gwamnatin kwarin gwiwar ci gaba da kula da hakkin da walwalar dakarun tsaron.

“Muna bukatar biyayya da goyon bayanku ga gwamnati da dokokin kasa, haka kuma ku yi kokarin ku yi watsi da duk wasu labaran rudu da ake yadawa a kafofin sada zumunta da kuma zantuka barkatai da jama’a ke yi a wurare daban daban wadanda suke cike da shirme, mu sojoji ne masu cikakkiyar da’a.”

Daga tarayyar Najeriya, Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)