logo

HAUSA

AU na kara azamar bunkasa sabbin sana’o’i a kasashen Afirka

2023-09-02 15:53:01 CMG Hausa

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, ta ce tana kara matsa kaimin ganin ta bunkasa ci gaban sabbin sana’o’i a sassan nahiyar Afirka. Wata sanarwa da sakatariyar kungiyar ta fitar a jiya Juma’a, ta ce sana’o’i mafiya kankanta, da kanana da matsakaita, su ne ke ingiza fannin kirkire-kirkire a Afirka, suna kuma taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa sabbin fasahohi, da samar da hajoji da hidimomi.

Wasu alkaluman da AUn ta fitar, sun nuna cewa, wannan rukuni na sana’o’i, su ne kashin bayan ci gaban tattalin arzikin Afirka, inda suke kunshe da kaso 80 zuwa 90 bisa dari, na jimillar sana’o’in da ake gudanarwa, kana suna bayar da gudummawar kusan kaso 85 bisa dari na kwadagon al’ummar nahiyar.

Sakamakon hakan, AU ta ce cikin matakan da take dauka a halin yanzu, ta shirya gudanar da taro shekara shekara karo na 2, game da sana’o’i mafiya kankanta, da kanana da matsakaita ko MSMEs, tsakanin ranaikun 4 zuwa 8 ga watan nan na Satumba, a helkwatar kungiyar ta AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha. (Saminu Alhassan)